DAGA MIMBARIN SALAFIYA NETWORK NIGERIA
DAGA MIMBARIN SALAFIYYAH NETWORK NIGERIA
!
Ash-Shaikhul Muhaddith!
Al-Allamatus-Salafiy!!
Abu AbdirRahman!!!
Muhammad Auwal Adam!!!
Albani Zaria!!!!
.
Allah Akbar!
Babban goro sai magogin 'karfe..
Allah ya karbi shahadarka.
ka hana bidia walwala.
Ka bayyana illolin Shia.
Ka bayyana illolin Boko haram
Anzo za'a gina coci a layin ka sai kace a'a bazai yiwu ba. An 'dauka cewa hayaniya za ayi sai kace a'a a gaya maka kudin filin cocin zaka siya. Allahu Akbar! Haka aka yi kuwa. Ana gaya maka kudin filin sai ka kawo kudin filin ka biya kace ka siya filin cocin ka mallakama makarantar Darul hadeethis Salafiyyah.
!
Allahu Akbar! 'Bangaren taimakon marayu ma ba'a barka a baya ba. Na tuna lokacin da marigayi shugaban izala Imam Ikara ya rasu. Garam ana zaune kace bazai yiwu ba a kawo maka wasu 'ya'yanshi ka basu scholarship a Albaniy Science Academy. Haka kuwa aka yi, ka 'dauko wasu 'ya'yanshi ka basu gurbin Karatu kyauta kace Imam Ikara ya bauta ma Sunnah don haka dole Da'awar Sunnah ta bauta ma 'ya'yan shi.
Ka bayyana asali da kuma makircin boko haram.
Ka bayyana illolin Allurar polio
W.H.O ta nemi ta baka cin hanci amma kaki amsa.
Ka Umurce ta da tazo ta 'karyata Prof Kaita amma taji tsoro.
.
'Bangaren taimakon malaman Sunnah tsofaffi ma ba'a barka a baya ba. Na tuna lokacin daka yima duk wani tsohon malamin Sunnah da 'karfinshi ya 'kare a Zaria albashi na naira dubu biyar ako wani wata. Su Mallam Ba'are kuwa da sauran malaman Soro har gida kake bunsu ka jinjina musu ka tallafa musu da kayayyakin masarufi.
!
Tsarki ya tabbata ga Allah! Na tuna lokacin daka taimaka ma su Mallam Najeeb El-Kabir Kwarbai da lauya a shari'arsu da 'yan shi'a. Mallam Najeeb El-Kabir yace min kuka ne kawai bai yi ba don farin ciki.
!
Ginin Daruul Hadethis SALAFIYYAH kuwa da littattafan ilimi ka kashe abunda bai yi 'kasa da naira miliyan 'dari (100,000,000) ba. Ka bar tafka-tafkan filayen da basu yi 'kasa da naira miliyan hamsin ba. Dukkannin wadannan dukiyoyin kace ka mallaka ma Da'awar Salafiyyah ne don haka kada wani jininka yazo yace yana da gado in kuma yayi haka toh Allah ya isa.
!
Ka ilmantar, ka fadakar akan duk wata barazana data fuskanto addinin Allah.
Ka kai gwauro ka kai mari wurin 'kokarin gina jami'a mai suna Grand Khadi Abubakar Mahmud Gumi University of Islamic Law amma Allah bai yarda ba. Fatanmu shine 'yan baya zasu cika maka wannan burin daka rasu dashi.
.
Allahu Akbar!
Wallahi Sardaunan malamai kai ba rago bane!
An kasa kayar da kai da ilimi sai dai da bakin bindigi. Bindigan ma sai a cikin duhu.
.
Makasan Mallam Kunji Kunya! Makasan Mallam kun taimaki Mallam wajen samun mutuwar Shahada (Insha'Allah)!! Makasan Mallam kun kashe maciji ne baku sare kanshi ba!!!
Kun kashe mallam ne amma baku kashe da'awarsa ba.
Daawa ba fasawa.
Fadin gaskia sai abin da yaci gaba. .
Allahu Akbar!
Makasan mallam kun makara.
Mallam ya zauna ya karantar da daliban ilimi.
Mallam yabar sadaka mai gudana. Mallam yace sai kun kariso yana jiranku gaban Allah asalilin dazai shaqo wuyarku ya gabatar daku a gaban Allah yace Ya Allah tambayesu me nayi musu suka kashe ni???????????
.
Munsan mallam ya tafi ba zai dawo ba.
Bama bukatar sanin wanda ya kashe mallam.
Mu dai fatanmu Allah yayi mashi rahma ya albarkaci zuriyarsa.
Ya kuma ba daliban sa ikon ci gaba daga inda yatsaya.
.
Ya Allah Al-Hayyu Al-Qayyum!
Allah ga da'awar Salafiyyah nan da Darul-Hadeethis-Salafiyyah Allah ka rike mana su da hannayenka na dama. Ya Allah duk wata fitina da ta taso a Darul-Hadeethis Salafiyyah Allah kashe mana ita ka kunyata makiyan Mallam da makiya Sunnah.
.
Makisa mallam Allah ya isa! Allah ya isa!! Allah ya isa!!!.
Comments
Post a Comment